FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya tambayi ‘yan Najeriya kan inda Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ke samun kudin da zai biya ma’aikatan jiharsa mafi karancin albashi na N70,000.
Legit ta ruwaito a baya cewa gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa biyan N60,000 a matsayin mafi karancin albashi ba zai yiwu ba kuma ba zai dore ba daga wurinsu.
Kara karanta wannan
Mafi karancin albashi: Shehu Sani ya yiwa N62,000 da gwamnati tayi ga ma'aikata fashin baki
Sani ya yi wannan tambaya ne bayan da gwamnonin jihohi suka ki amincewa da tayin karin mafi karancin albashi zuwa N60,000 da gwamnatin tarayya ta gabatarwa Kungiyoyin kwadago.
Ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X, @ShehuSani a ranar Asabar, 8 ga watan Yunin wannan shekarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Daga ina jihar Edo ke samun kudinta da za ta tabbatar da daga mafi karancin albashi zuwa N70,000?”Legit ta tattara wasu daga cikin martanin 'yan Najeriya game da biyan mafi karancin albashi na N70,000 ga ma'aikatan jihar Edo.
@official_osasb7 ya ce:
"Wannan kyauta ce ta yaudara saboda zaben gwamna na jihar Edo yana nan gabatowa cikin wata uku."@iammegaken ya ce:
"Jihar Edo ita ce ta fara biyan N40,000 shekaru biyu da suka wuce kafin ta kara zuwa N70,000 a wannan shekarar."Kara karanta wannan
Mafi karancin albashi: 'Yan Najeriya sun gano tushen matsalolin kasa, sun ambaci suna
@valencia_cute5 ta ce:
"Kowace jiha a Najeriya za ta iya biyan fiye da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi idan an so, amma son zuciyar ‘yan siyasa da son kai ba zai bar su su yi abin da ya dace ba, maimakon haka za su ta ba da uzurin karya don rufe gaskiyarsu."@UIlawagbon ya ce:
"Wa’adin mutum zai kare cikin wata uku yana daga mafi karancin albashi zuwa N70,000. Wa yake kokarin yaudara!"@waltskillslfc ya ce:
"Gwamnan na kokarin haifarwa sabon gwamna matsala ne kawai."@tjawiee ya ce:
"Ina ganin zai iya zama alheri ga kasa idan aka yi la’akari da hada jihohin da ba sa tabuka komai wuri daya."A wani labarin, tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan sabon tsarin gwamnatin tarayya na mafi karancin albashin ma'aikata na N62,000 a kasa baki daya.
Kara karanta wannan
NLC: Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya kawo mafita kan mafi ƙarancin albashi a jihohi
Legit ta ruwaito cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta kara tayin sabon mafi karancin albashin ma'aikata zuwa N62,000 daga N60,000.
Adadin ya tabbata ne yayin da batun ya fito daga bakin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC masu ci (PGF).
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboN1gY9mmGahnpZ6qMPApqWapl2asbB52JpkoJldo4RxfI9pZKeZXaKup7WMpJirmZ6Ytq95wKWZmquYnnq0tMShrGaxkWLBor%2FOZp6wmZ2jvK%2B1jJpkoJmSlnw%3D