Abuja - Ismail Maiduguri ya tofa albarkacin bakinsa game da halin da Najeriya take ciki a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu.
Alhafiz Ismail Maiduguri ya ce a yanzu ‘yan siyasa sun fahimci cewa za a iya yin amfani da abin duniya a saye kuri’u lokacin zabe.
Wani bidiyon malamin a shafin X ya nuna shi yana bayanin yadda aka yi amfani da taliya wajen samun goyon bayan talaka a bara.
Kara karanta wannan
Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga talakawa, ya ce masu mulkin yau sun yi amfani da dukiyarsu wajen rufa bakin wasu malaman addinin musulunci da kirista.
Wannan malami ya ce ba a taru an zama daya ba, amma akwai jagororin addini da suka cefanar da matsayin da Ubangiji ya ba su.
"Akwai malamanku da fastoci da ke cewa a zabi wane da kyakkyawar niyya. Amma akwai da yawa da ciniki ake yi da su.""Iyakar yawan masu yi masa (malami) kabbara ko halleluiah a coci, iya yawan kudin da za a ba shi (Fasto, Fada ko Rabaren)."- Ismail Maiduguri
Ismail Maiduguri ya yi ikirarin bayan zabe ba a jin wani ya fito ya ce uffan saboda kudi ne suka yi aiki wajen samun shugabanci.
Kara karanta wannan
InnalilLahi: 'Yan bindiga sun bindige ma'aikacin FIRS a tsakiyar birnin Abuja
Malamin yake cewa ko da farashin man fetur ya tashi, sai dai a ji masana addini suna fadawa talaka ya kara hakuri kuma ya tuba.
Bayanan sun zo ne a wajen karatun littafin da ya fara game da tarihin mata da mazan da ka kewaye da Annabi Muhammad SAW.
Sa’ad Yusuf Abu Azeez ya rubuta fitaccen litafin da malamin yake karantarwa a masallacin Zone B a rukunin gidajen ‘yan majalisu.
Sai dai Ismail Maiduguri yana ganin akwai laifin talaka domin ba tursasa masa aka yi, shi da kan shi ya zabi wadanda aka tallata masa.
An ji labari babban malamin nan, Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya ce talakawa suna shan wahala a gwamnatin APC mai-mulki.
Adamu Muhammad Dokoro yana so shugabanni su gama lafiya, ba wai su gama da talakawansu ba ganin ana cikin kuncin rayuwa.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ6fZhramaZnJa%2ForrMmmSymameerW7zailZquZobattYyymGablWLBqrrUm6xmsZFiwKLFxGaqoZ2YqruitYysn6Kxkaiubq3KmmSjoV2pwKrAjJpkspmlZA%3D%3D