Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Cross River - Rundunar yan sanda ta sanar da kama jami'inta da yake zaman kansa kimanin shekaru 10.
Ana zargin dan sandan mai suna Buba Adamu da cigaba da aiki ba tare da tafiya a karkashin rundunar yan sanda ba.
Kara karanta wannan
Sojojin Najeriya sun ragargaji 'yan ta'adda a jihohin Kudu
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana zargin dan sandan da aikata ayyukan ta'addanci a wasu yankunan jihar Cross River.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar yan sanda a jihar Cross River ta sanar da cafke jami'anta da aka canzawa wajen aiki amma ya ki zuwa, ya fara zaman kansa.
An ruwaito cewa an canzawa jami'in mai suna Buba Adamu wajen aiki daga Cross River zuwa Kaduna tun a shekarar 2015 amma yaki tafiya.
Bayan kin tafiya garin da aka tura shi, dan sandan ya cigaba da aiki a jihar Cross River tare da karawa kansa matsayi, rahoton The Guardian.
Ana zargin cewa dan sandan ya karawa kansa matsayi daga kofur zuwa sufeton yan sanda (SP) cikin shekarun da yake zaman kansa.
Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi aika aika a Imo, sun kashe 'yan sanda da farar hula
Kakakin rundunar yan sandan jihar Cross River, SP Irene Ugbo ya ce ana zargin jami'in da aikata ayyukan ta'addanci.
SP Irene Ugbo ya ce akwai alamu da suka nuna ya aikata ta'addanci a yankin Bococo da Nasarawa kuma za a cigaba da bincikensa har sai an gano gaskiya.
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan matsalar rashin tsaro a ƙasa da ke ƙara taɓarɓarewa.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai huta ba har sai ya kawo ƙarshen duk wasu masu hannu kan matsalar rashin tsaron.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboR0hZFmmKdlm5a6onnDmqVmq5GjsaK6jJ2YZrGRYsCprcWeZKyglaCus8GMpKCmmZ6eu259j2awmqaRYseiucCnZKSZnqiucA%3D%3D