Bauchi - Shehu Umar Buba mai wakiltar kudancin Bauchi a majalisar dattawa, ya yi karin haske game da aikin hako mai a Kolmani.
Daily Trust ta ce Shehu Umar Buba ya ce kamfanin NNPCL sun yi alkawarin cigaba da yunkurin samar da mai daga rijiyoyin Kolmani.
Sanata Shehu Umar Buba ya yi wannan bayani ne da yake amsa tambayoyi a wajen manema labarai ranar Litinin a garin Bauchi.
Kara karanta wannan
Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan majalisar ya ce masu ruwa da tsaki a Bauchi da Gombe sun damu da lamarin rijiyoyin man da aka gano a shekarun nan.
Shehu Umar Buba wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattawa ya ce yana zuwa majalisa ya fara bijiro da batun man.
Sanata Shehu Buba yake cewa sun nemi jin dalilin da ya sa aikin ya tsaya tun bayan da Muhammadu Buhari ya kaddamar a 2022.
An rahoto Sanatan yana bayanin yadda suka yi zama da jami’an gwamnatin tarayya da ‘yan majalisu domin farfado muhimmin aikin.
Kara karanta wannan
An shiga jimami bayan rasuwar shahararren jarumin fina-finai a Najeriya da shekaru 81
"Mun bukaci sanin meyasa tun da tsohon shugaan kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da rijiyoyin man, aka yi watsi da ayyuka a wurin.""Shugaban NNPC ya ba mu bayanai masu gamsarwa. Yanzu NNPC ya bada kwangila ga wani kamfanin Indiya da sun shigo kasar, ana ta shirye-shirye."- Shehu Usman Baba
A watan nan za a fara aiki, idan Fabrairu ta wuce shiru, Sanatan ya ce za su fito fili su yi magana kuma za su yi amfani da zauren majalisar tarayya.
A karshen 2022 aka ji labari Muhammad Buhari ya hallara kauyen Kolmani domin a fara aikin hako danyen mai a karon farko a Arewa.
Kwatsam sai aka ji wani Abdullahi Tamatuwa yana yi wa jihar Bauchi barazanar cewa zai je kotu, ya ce rijiyoyin a Gombe suka fada.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbIRzg5RmmKdlo52yrK3RmmRqZaOdtrPBjKyYp5mklnq6rYyfmJ2hXZ2urbXNZpuaZZGgsm6vyKSgZq%2BRn7KveceaoqhllJa7urHNZqSaoV2WeqK%2BxLCYaA%3D%3D