Miyetti Allah Kautal Hore, kungiyar makiyaya, ta goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu a zaben 2023.
The Sun ta rahoto cewa goyon bayan na zuwa ne bayan tattaunawa mai tsawo tsakanin kungiyar makiyayan da wakilan dan takarar shugaban kasa na APC wacce aka kamalla a baya-bayan nan.
Kara karanta wannan
Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance Tsakanin APC, PDP, LP da NNPP a Jihohi 36
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma tattaro cewa an cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu an rattaba hannu cewa za a yi aiki tare don tabbatar da cewa dan takarar shugaban kasa na APC ya ci zabe ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.
Da aka tuntube shi, shugaban kungiyar, Alhaji Bello Bodejo, ya tabbatar da cigaban, ya kara da cewa a ranar Juma'a kungiyar za ta sanar da goyon bayanta ga Tinubu a hukumance a taronta da za a yi a Lafiya.
Ya ce:
"Muna da babban taron mutanen mu, makiyaya fulani, da za a yi a ranar Juma'a a Lafia. A wurin taron ne za mu sanar da hukumance cewa Tinubu ne zabin mu na shugaban kasa. Idan za ka iya tunawa, makonni da suka gabata mun ce za mu sanar da dan takarar shugaban kasar mu a zabe mai zuwa kuma abin da za a yi ranar Juma'a kenan.Kara karanta wannan
Magoya Bayan Jonathan Sun Tsaida ‘Dan Takara, Sun Shiga Yi wa Tinubu Kamfe a Kudu
"Mun zauna da wakilai mun tattauna sosai kan dalilan da zai sa mu goyi bayan, bangarorin biyu sun gamsu da abin da aka cimma. Mun kuma rattaba hannu, an gama komai. Zamu fitar da wasu bayanai idan bukatan hakan ya tashi."A wani rahoton, Sunday Asefon, shugaban kungiyar Tinubu/Shettima Vanguard ya yi alkawarin tattaro kan daliban Najeriya su goyi bayan Tinubu a zaben 2023.
Kamar yadda The Nation ta rahoto, Asefon ya yi alkawarin ne a wurin kaddamar da kungiyar Tinubu/Shettima Vanguard.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJyfZZqbmaZpJ64tnnToqWumqViuLB5zpugZpyRnK5ut8CrqqGdXaK2urHTraBmmZyhrql505pkm5mprq6vrYydmKdlpJa4or7Aq2SsoKWcrqOtzWaimquRYrGiedmaZK2ZXa%2Buo62O