Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce babu wanda ya isa ya tuhumi Allah kan kowane irin lamari da ya aiwatar.
Basaraken ya faɗi haka ne a hudubar Sallar Jumu'a da ya gabatar a babban masallacin Jumu'a na Ƙofar Kudu a jihar Kano a yau.
Kara karanta wannan
Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hudubar Sarkin ta yau ta maida hankali ne kan imani da Allah a kowane yanayi mutum ya tsinci kansa, na farin ciki ko jarabawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Muhammadu Sanusi II.
Kara karanta wannan
"Dalilin da ya sa har yanzu Aminu Ado Bayero yake halastaccen Sarkin Kano"
Bayan haka ne mai martaba sarkin ya jagoranci Sallah raka'a biyu ta Jumu'a a masallacin fadar Ƙofar Kudu.
A ɗazu rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta musanta rahotannin da ke cewa Ado Bayero zai jagoranci Sallar Juma’a a babban masallacin Kofar Kudu da ke Kano.
Sanusi II da Aminu Ado Bayero su na da'awar su ne rike da iko, lamarin da ya haifar da rudani a cikin birnin Kano.
Rikicin sarautar dai na ci gaba da ƙamari tun bayan dawo da Sarki Sanusi II da kuma rusa masarautun nan biyar.
A wani rahoton kuma wani lauya a jihar Kano, Umar Sa'ad Hassan, ya yi bayanin cewa har yanzun Alhaji Aminu Ado Bayero ne halastaccen Sarki.
Umar Hassan ya bayyana cewa babbar kotun tarayya mai zama a jihar ta ba da umarnin dakatar da mayar da Muhammadu Sanusi kan sarauta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboJyg5ZmmZplp5a7pa2Ms5iiZZqWeqWtjKGspK2emLavecClo5qgXaius7fIZqqapqWotm7FwGahmmWYlrusrcuiZJplmKqxtq7Aq2SjrZ2qrql7