Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Shugaban karamar hukumar Ikwerre a jihar Rivers, Dakta Samuel Nwanosike ya sha alwashin ci gaba da zama a kujerarsa.
Nwanosike ya gargadi Gwamna Sim Fubara kan shirin da ya ke yi a kansu inda ya ce babu mai cire shi a kujerarsa.
Kara karanta wannan
"Ina godiya Abba": Sarki Sanusi II ya magantu bayan dawowa kujerarsa
Shugaban karamar hukumar ya ce shi bai aminta da wa'adin da gwamnan ya ba su na ranar 16 ga watan Yuni ba a cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya dauki matakin ne ganin karin wa'adi da aka yi musu a Majalisar jihar karkashin jagorancin Martin Amaewhule, Punch ta tattaro.
Hakan ya biyo bayan ƙarin wa'adin da majalisar ta yi ga shugabannin ƙananan hukumomin saboda rashin gudanar da zabensu a jihar.
Har ila yau, Nwanosike ya ce zai ci gaba da kasancewa kan kujerarsa har zuwa lokacin da wa'adinsa da majalisar ta ba su ya kare.
Ya gargadi mutanen yankin Ikwerre da kada su bari wani ya fara yunkurin cire shi daga mukaminsa na shugaban karamar hukumar.
"Saura kwanaki 23 su zo su ce za su cire ni su gani idan sun isa, ku zo ku nuna rashin bin doka. Mu doka muke bi wanda Martini Amaewhule ya tabbatar, idan kun haifu ku zo."Kara karanta wannan
Abba ya tabbatar da korar Aminu Ado Bayero, ya sanya hannu a dokar da ta rusa su
"Idan Amaewhule ya tabbatar cewa umarnin da ya bayar shi ne in ci gaba da kasancewa a ofis, shikenan zan zauna, wannan ita ce dokar jihar Rivers."- Samuel Nwanosike
Kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya yi alfahari kan irin ayyukan ci gaba da ya kawo jihar Rivers a cikin shekara daya.
Fubara ya ce ayyukan alheri da ya yi a dan kankanin lokaci yafi na gwamnatoci da dama da suka shafe shekaru takwas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ6gI9wamaakZfCbrnAomStp6Odsm65yKdkoZmerq6zecCboKebmWLAqcHGmpmapl2grrOtzJqpZqCloMKurYyymGaZl5Z6uq3TrJhmn5FitLitzKeYp6uRZA%3D%3D