A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano -Jam'iyyar APC a Kano ta ce babu wanda zai shiga jam'iyyar face Shugabanta, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sa masa albarka.
Kakakin jam'iyyar a Kano, Ahmed S Aruwa ne ya shaidawa Legit Hausa hakan a yammacin Alhamis.
Kara karanta wannan
Jam'iyyar APC ta yi magana kan umarnin kotu, ta faɗi mutanen da suka dakatar da Ganduje
'Dan siyasar ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kaunar Dr. Ganduje, kuma babu wanda zai taba alakarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake magana ka labarin yana zargin gwamnatin tarayya da kokarin tunbuke Dr. Ganduje daga mukaminsa, Ahmed S Aruwa ya ce sharri ne irin na 'yan adawa, domin suna biyayya ga fadar shugaban kasar.
"Wannan kalma ce kawai ta 'yan adawanmu da muke da ita a nan Kano."- Ahmad Aruwa
Ya ce labarin da ake yayatawa ya dade sosai, wanda yana magana ne kan jagoran kwankwasiyya dake kokarin hada kai da wasu a fadar shugaban kasa domin yi wa shugabansa zagon kasa.
Ahmed S Aruwa ya zargi jagoran NNPP, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da kunno wutar rikici a jam'iyyar APC saboda baya son zama inuwa guda da Ganduje a shirinsa na dawowa jami'iyyar.
Kara karanta wannan
Dakatar da Ganduje: Jam'iyyar APC ta mayar da martani kan hukuncin babbar kotun Kano
Ya ce:
"Mun je mun yi bincike mun gane 'yan kwankwasiyya ne, mutanen NNPP ne.""Kuma mun kai kara, kuma mun turawa 'yan sanda, mun turawa daraktan tsaro, in Allah SWT ya yarda wadannan yaran, za a kamo su, za a kai su gaban kuliya."Kakakin APCn ya ce ba su bukatar Kwankwaso da jama'arsa su dawo APC matukar rikici za su taho da shi.
Tun bayan dambarwar da ta faro da ayyana korar tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje daga jam'iyyar APC ne shugaban ke ganin babu mai iya jijjiga shi.
A sakon da ya tura ga 'yan adawa, Dr. Ganduje ya bayyana cewa ya riga ya sha gabansu, saboda haka magana ce kawai ake amma babu abin da zai taba kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar APC ta kasa.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ5hJRva2aakZfCbsPAp5uaZZGeerS0yKCmZpmgmHq0rchmm5plma%2B2r7XNZp6appSqt6Z5wKussJlf