Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Borno - Wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’addan Boko Haram ne da suka tuba sun sake daukar makamai yayin da suka farmaki jami'an tsaro a jihar Borno.
An ruwaito cewa sun kona shingayen binciken kwakwaf na hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da hukumar kwastam ta Najeriya (NCS).
Kara karanta wannan
"Sako ga masarautar Zamfara": 'Yan bindiga sun saki bidiyon hadimin sarki da suka sace
Zagazola Makama, wani mai sharhi kan al'amuran ta'addanci a yankin tafkin Chadi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makama ya rahoto cewa tubabbun 'yan Boko Haram din sanye da kakin sojoji sun mamaye Kasuwar Fara a Maiduguri inda suka fatattaki jami'an hukumomin.
Ya ce ‘yan ta’addan sun kona dukkanin shingen binciken, inda suka koma ofishin ‘yan sanda reshen Kasuwar Fara da yunkurin sakin mambobinsu takwas da ke tsare.
Makama ya ce an kama wadanda ake tsare da su ne a ranar 24 ga watan Afrilu yayin wani samame da ‘yan sanda suka kai a wani kauye mai suna Kasuwan Fara, in ji jaridar The Cable.
Mai fashin bakin ya ce jami’an ‘yan sandan sun yi artabu da ‘yan ta’addan, inda ya kara da cewa an fi karfin ‘yan ta’addan lamarin da ya tilasta su guduwa daga wurin.
Kara karanta wannan
Kano: Dilan wiwi da 'yan sanda ke nema ruwa a jallo ya shiga hannu
Ya ce kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Kenneth Daso, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo maharan.
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa ma'aikata a jihar Borno sun koka kan Naira 4,000 da wasu tsofaffin ma'aikata ke karba a matsayin kudin fansho a wata.
Kungiyar kwadago reshen jihar yayin da take rokon Gwamna Babagana Zulum da ya duba lamarin ta yi nuni da cewa babu abin da kudin za yi a wannan yanayin na tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbn13gJJmmaiqnqR6tcHBmpmbrZ5ixqK6jJumpKddna6zrcxmqq6mXaiurLGMnZiuo5Gneq6typqkmqFdqMKvecWaqaajkaC2brbApqBmrKOWv7B7