Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan Yaro bisa rasuwar babban dan kasuwa kuma mai taimakon al'umma, Alhaji Ahmadu Yaro.
Sanarwar da ta fito daga mai magana da yawun shugban kasa, Garba Shehu ta ce shugaban kasa kuma ya mika ta'aziyarsa ga tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya, Ibrahim Salisu Buhari bisa rasuwar mahaifinsa, Alhaji Salisu Buhari Daura.
Shugaban kasar ya ce daya daga cikin halayen Yaro shine mayar da hankali wurin sana'a da kuma bayar da dukiyarsa wurin gudanar da ayyukan cigaba a garinsa da ma wasu garuruwan.
DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka
Ya ce: "Ya kasance gogagen dan kasuwa ne da ya yi zama sosai a birnin Legas. Yaro dan Najeriya ne na gaskiya wanda ya kasance a kullum yana goyon bayan zaman lafiya da cigaba da sassan Najeriya."
A yayin da ya ke mika ta'aziyarsa ga al'umma da gwamnatin jihar Jigawa da 'yan kasuwa bisa rasuwan Najeriya bisa rasuwar dattijo kuma mai taimakon al'umma, Shugaban kasar ya yi addu'ar Allah ya bawa iyalansa, abokansa da abokan aikinsa juriyar rashinsa.
Ya kuma yi addu'ar Allah ya jikansa da rahama ya saka masa da gidan aljanna kamar yadda kamfanin dillancin labarai, NAN ta ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kWxobG1jYq%2B2tMCroGaxkWLGqnnApZ%2Bippmjeq7B066umqpdlrWurcOuZLKZoqR6pa2MrJiloaOqeqPBx5qpomaYqbqt