Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Shugaban New Nigeria People’s Party (NNPP) reshen jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa ya musanta rahoton cewa EFCC ta taso Rabiu Kwankwaso a gaba.
Dungurawa ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa hukumar yaki da rashawa EFCC ta fara bincikar Kwankwaso kan wasu kuɗin kamfen NNPP.
Kara karanta wannan
EFCC ta fara binciken Sanata Rabi'u Kwankwaso kan zambar kudin 'yan fansho
Ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a birnin Kano, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dungurawa ya bayyana rahotannin da ake yaɗawa a matsayin marasa tushe, inda ya ce Kwankwaso mutum ne amintacce kuma mai gaskiya.
Ya ce:
"Mun sha ganin irin wannan jita-jita a lokuta daban-daban kuma ba zamu hana su ba, su ci gaba da yaɗawa."Ko sun so ko ba su so, Kwankwaso ne mutum daya tilo da ya rage mai gaskiya, mutunci, farin jini, da gogewar mulkin kasar nan.”Shugaban NNPP na Kano ya yi fatali da rahoton binciken EFCC, yana mai bayyana shi da labari mara tushe wanda ƴan adawar Kwankwaso suka ƙirƙiro domin ɓata shi.
Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya nuna gwamna 1, ya buƙaci sauran gwamnoni su yi koyi da shi
A cewarsa, wannan rahoton ƙaryar ya taso ne daga ɓangaren masu adawa da Kwankwaso, waɗanda ba su ƙaunar ya zama shugaban ƙasa.
Dungurawa ya tabbatar da cewa babu wani zarge-zargen zamba, rashin da’a, almubazzaranci, ko satar dukiyar al’umma a kan Kwankwaso, rahoton Vanguard.
A wani rahoton kuma wasu fusatattun mambobin jam'iyyar APC mata sun mamaye hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja ranar Jumu'a.
Dandazon matan sun gudanar da zanga-zanga ne domin nuna rashin jin daɗinsu da halin shugabar matan APC Mary Alile-Idele.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ6gZFscGadlpiwbrrAZpmippOeuKa6jKSumqabrK60u4ykmKuxkWK7pnnSoaygmZKWu266zamnZqaRYriius5o