Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar ICPC ta gurfanar da wata mata kan zargin sa hannun jabu na marigayi Abba Kyari.
Kafin rasuwarsa, Kyari ya rike mukamin shugaban ma'aikatan gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Hukumar ta ICPC ita ta bayyana haka a yau Lahadi 12 ga watan Mayu a shafinta na Facebook.
Kara karanta wannan
Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wacce ake zargin Ramat Mercy Mba mai 'ya'ya biyar an gurfanar da ita a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Alkalin kotun, Mai Shari'a, Ibrahim Mohammed ya dage yanke hukuncin zuwa ranar Alhamis 16 ga watan Mayu.
Sai dai alkalin kotun ya ba da umarnin ci gaba da tsare ta a gidan kaso da ke garin Suleja a jihar Niger kafin ranar yanke hukuncin.
Hukumar ICPC ta gurfanar da Mercy Mba tun a watan Yunin 2022 kan tuhume-tuhume har guda biyar a kotun.
Daga cikin zarge-zargen akwai cin amana da damfara da kuma sata wanda ya sabawa sashe na 13 na dokokin hukumar.
Har ila yau, laifuffukan sun sabawa sashe na 320 da kuma 366 na manyan lafuffuka na Arewacin Najeriya.
Kara karanta wannan
Majalisa ta amince da karin albashi ga wasu ma'aikata, an fadi yawan kuɗin
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta kama kwamandan hukumar tsaro ta NSCDC, Christopher Oluchukwu bisa zamba.
An samu Kwamandan da laifi ne bayan an gurfanar da shi a gaban babbar kotun jihar Katsina bisa karban makudan kudade a wurin wasu mutane uku.
Rahotanni sun tabbatar cewa an kama shi da laifin karban kudade daban-daban wadanda suka hada da N200,000, N300,000 da kuma N400,000.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbn9xfpFmoJyok2LBonnGrqmfmZ6Wv26wwGabmqyknre2w8BmopqmXaiubrTAp6Wupl2frqPBjKeYZqWRp7aordiiZJqakpZ6rMXAq6Bo