Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Neja - Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (NSEMA) reshe jihar Neja ta bayyana cewa na samu rahoton hatsarin jirgin ruwa a jihar.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Borgu da ke jihar inda mutane fiye da 100 suka nitse a cikin ruwa, cewar Daily Nigerian.
Kara karanta wannan
Ana ci gaba da kuka kan sace 'yan mata a Abuja, 'yan bindiga sun kuma sace wasu 45 a Benue
Babban Daraktan hukumar a jihar, Abdullahi Baba-Arah shi ya bayyana haka a yau Litinin 15 ga watan Janairu a Minna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baba-Arah ya ce lamarin ya faru a yau Litinin 15 ga watan Janairu da rana bayan tashi daga Dugga Mashaya zuwa kasuwar Wara a jihar Kebbi.
Ya ce jirgin ruwan na dauke da fasinjoji da akalla suka kai guda 100 dauke kuma da wasu kayayyaki, Leadership ta tattaro.
Sauran abubuwan da ke ciki sun hada da hatsi da sauran kayayyaki masu amfani da fasinjojin suka dauko.
Ya kara da cewa hukumar har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba ta iya sanin adadin wadanda suka mutu da masu rai ba.
Mista Abdullahi ya ce yanzu haka an bazama zakulo wadanda abin ya rutsa da su daga direbobi da sauran jami'an hukumar.
Kara karanta wannan
Jimami yayin da mahara suka kona fadar babban Basarake kurmus, ya koka kan lamarin
A wani labarin, an samu mummunar labarin cewa wasu mata da kuma yara sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a rafin Neja.
Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Disamba yayin da aka gano mutane na kokarin ceto su.
Jihar Neja na yawan fama da hatsuran jragen ruwa wanda ya yi ajalin mutane dama a jihar.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbIB3gJVmoaKql567br7UsJhmnJGquKZ5w5pkn5mjnruru8miZGpoYGLGonnKop2eZZFiu6a2wGalrJ2dlnw%3D