Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Kungiyar Arewa Think Tank ya caccaki malamin addinin Musulunci kan kalamansa ga matar Shugaba Tinubu.
Kungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da dakatar da malamin daga gudanar da wa’azi saboda ya zama izina ga sauran malamai, cewar Leadership.
Kara karanta wannan
Atiku ya karantar da Tinubu, ya fadawa Shugaban kasa hanyar gyara a saukake
Idan ba a manta ba, wani malami daga jihar Sokoto ya bayyana cewa ya kamata a hallaka Remi Tinubu saboda kasancewarta Kirista.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar, Muhammad Yakubu shi ya bayyana haka a karshen mako inda ya ce akwai hakkin caccakar gwamnati amma ba ta wannar hanya ba.
Ya ce kiran kisan matar shugaban kasa abin Allah wadai ne kuma ba za a taba amincewa da hakan ba, cewar Arise TV.
Kungiyar ta kuma bukaci a hukunta malamin dai-dai da abin da ya aikata don hakan ya zama izina ga sauran malamai.
A cewar sanarwar:
“Mu a Arewa Think Tank mun yi Allah wadai da kalaman malamin kan ga maar Tinubu, Oluremi Tinubu saboda addininta.“Malamin ya kauce wa tsarin koyarwar Musulunci, mu addininmu ya koya mana yadda za mu zauna da wasu lafiya cikin al'umma.Kara karanta wannan
El-Rufai ya magantu kan malamin Musulunci da ya nemi a hallaka Remi Tinubu kan wani dalili
“Muna kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar sun hukunta wannan malamin, kowa ya na da hakkin sukar gwamnati amma kiran a hallaka mai daraja a cikin al’umma ya saba doka.”Kun ji cewa dan Majalisar Tarayya a Najeriya, Muhammad Bello El-Rufai ya yi martani kan malamin da ya zagi matar Tinubu.
Bello ya ce ba a bukatar neman afuwar malamin inda ya bukaci a hukunta malamin kan kalamansa ga Remi Tinubu.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbX13g5Jmoq6ml57GonnAZpirnaeWerWtjJ%2BYnaFdlq%2BquoydmGaxkWK4ornArZhmrJmjwqPBjLKYZrGZYsSiecyao5qlmaN6pa2MsphmspGctm65wK2Yq6uRYsGiecWam6JllJa5qrjIaA%3D%3D