Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake duba manufofinsa kan tattalin arziƙin ƙasar nan.
Ƙungiyar ta yi nuni da cewa manufofin shugaban ƙasar nan kan tattalin arziƙi sun jefa ƴan Najeriya cikin talauci.
Kara karanta wannan
Kungiyar sarakuna ta ba Sanusi II shawara kan rikicin masarautar Kano
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar, Justice Faloye ya fitar, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar Afenifere ta caccaki manufofin Shugaba Tinubu kan tattalin arziƙi.
Afenifere tayi nuni da cewa abubuwa sun ƙara taɓarɓarewa fiye da lokacin gwamnatin da ta gabace shi, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Ƙungiyar ta bayyana cewa a cikin shekara ɗaya ta gwamnatin Tinubu, tattalin arziƙin ƙasar nan ya shiga halin ƙaƙaniƙayi fiye da lokacin gwamnatin baya.
Ƙungiyar ta kuma caccaki cire tallafin man fetur da mayar da farashin canjin kuɗi na bai ɗaya, inda ta ce waɗannan matakan sun taimaka wajen taɓarɓarewar tattalin arziƙi da jefa ƴan Najeriya cikin wuya.
Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta fahimci tattalin arziƙin ƙasar nan ta yadda za ta rage hauhawar farashin kayayyaki, rashin aikin yi, rashin matsuguni da talaucin da ake fama da shi.
Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta dawo da shirin rage talauci ga 'yan Najeriya miliyan 75
Ta buƙaci gwamnati da ta janye tsarin cire tallafin man fetur da yawan jibga haraji kan ƴan Najeriya.
Ta yi nuni da cewa waɗannan manufofin sun taimaka wajen taɓarɓarewar tattalin arziƙi wanda hakan ya jawo hauhawar farashin kayayyaki da raguwar kuɗaɗen shiga da mutane ke samu.
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan kudirin dokar taken Najeriya da majalisar dokokin tarayya ta zartar.
Rattaɓa hannun da shugaban ƙasan ya yi kan sabon ƙudirin ya sanya za a dawo da yin amfani da tsohon taken Najeriya na “Najeriya, mun jinjina miki”.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboF5hZNmoq6ml57Gor6MspirmpGsrm7AwGaampuTlriqedKao6imXaLCrbfIp2StoZ6qr7Z505pkpJmnpHqurcWiq5pn