Jihar Ogun - Shugabanni da magoya bayan tsagin tsohon gwamna Ibikunle Amosun daga ƙananan hukumomi 20 sun hakura, sun koma inuwar APC ta tsagin gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun.
Gwamna Abiodun da kansa ne ya karɓi waɗan da suka dawo cikin jam'iyyar APC ta asali ƙarƙashin jagorancin shugaban na tsagin Amosun ranar Jumu'a.
Channels TV ta ce yayin da yake maraba da dawowarsu a Abeokuta, Gwamnan ya yaba musu bisa mubaya'ar da suka yi masa a matsayin jagoran APC na jihar Ogun.
Kara karanta wannan
Shekaru 4 Masu Kyau Sun Fi Wa’adi 2 Mara Amfani, Inji Gwamnan PDP
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abiodun ya ce:
“Ina mai taya ku murna bisa ga wannan biyayyar da kuka yi ga shugabanci wanda zan ce ba abin a yaba ne kawai ba, ya fi ƙarfin a kushe shi ta kowane fanni.""Wasu kuwa guduwa suke da zarar abubuwa ba su tafi da kyau ba, amma ku kuna nan, ba inda kuka je, wannan biyayya ta kai maƙurar abin koyi. Dole ne mu aminta da cewa shugaba daya ne ake iya samu a jam’iyya lokaci guda.""A matsayina na jagoran jam'iyyar mu, na san nauyin da aka ɗora mun, kuma haƙƙi ne a kaina na yi aiki domin walwalar mambobin jam'iyya gaba ɗaya."Ya kuma bukaci daukacin mambobi da su manta da abubuwan da suka faru a baya, su haɗa hannu wajen sake gina APC don cimma manufofinta da bunƙasa tattalin arzikin Ogun.
Kara karanta wannan
Ana Tsaka da Yanke Hukunci a Kotunan Zabe, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC
A nasa jawabi, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Yemi Sanusi, ya ce a kowace alakar dan Adam zo mu zauna ne zo mu saɓa, kamar yadda PM News ta tattaro.
Amma ya yi imanin cewa, ko a lokutan yaki, a ko da yaushe akwai wurin da za a sasanta rikicin cikin lumana, yana mai kira ga wadanda suka dawo da su hada kansu da sauran ‘yan jam’iyyar.
Shugaban wadanda suka dawo, Derin Adebiyi, ya ce dukkansu sun amince su koma inuwar APC ne don bayar da tasu gudunmawar ga ci gaban jam’iyyar da jihar baki daya.
A wani rahoton kuma Ɗan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar SDP a jihar Ekiti, Ladi Owolabi, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Owolabi ya samu tarba hannu bibbiyu daga shugaban APC na gundumarsa, Ojo Adeyanju, tare da wasu mambobin jam'iyyar.
Kara karanta wannan
Gwamnan PDP a Arewa Ya Maida Martani Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a 2023
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ2gZJuaGanl6q7br%2FHrp6ampGju6q6jK2qmp%2BZo3qiuc6srKdlo6q7brTAnZxmnJFirqO1zp2sp2WRYq6xr44%3D