Mujallar Forbes ta Amurka ta fitar jerin ýan wasan da suka fi samun kudi ta shekarar 2023.
Jerin sunayen ya bayyana albashin ‘yan wasan ba tare da haraji ko alawus ba da kuma tallace-tallace.
Mujallar ta bayyana cewa ‘yan wasa 10 da aka fitar a jerin rahoton suna diban akalla $1.11bn ba tare da haraji ko sallamar wakili ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gobarar titi: Gwamnati ta raba wa wadanda aka kwaso daga Sudan N100k, katin N25k da data 1.5GB
Rahoton ya fayyace $20m da kuma 12% daga shekarar da ta gabata na $990m, sannan karin 5% na $1.6bn da aka samu a shekarar 2018.
‘Yan wasan kwallon kafa ta Amurka su suka mamaye jerin sunayen ‘yan wasan motsa jiki .
Jerin sunayen ya kunshi ‘yan wasan motsa jiki 10, da ‘yan wasan kwallon kafa da kuma kwallon kwando su suka mamaye jerin sunayen, in da na gaba-gaba ke dauke da ‘yan wasan kwallon kafa 3.
Bayan ya sauya sheka zuwa kasar Saudi Arabia, Cristiano Ronaldo shi ne akan gaba da kudaden shiga akalla $36m, sakamakon albashi na $75m.
Abokin hamayyarsa, Lionel Messi shi ne ke biye da akalla makudan kudaden shiga da yakai $130m.
Na ukun su shi ne jajirtaccen dan kwallon kafan Faransa, Kylian Mbappe da zunzurutun kudi $120m.
Jam’iyyun Adawa Sun Yi Taro, An Tsara Yadda Za a Yaki ‘Yan Takaran APC a Majalisa
A wani labarin, Mahaifiyar dan wasan kwallon kafan Maroko da PSG Achraf Hakimi, Saida Mouh ta yi martani game da jita-jitan cewa danta ta maka sunanta kan dukkan kadarorinsa.
A cewar Saida, bata san da hakan ba, kuma bata shirya hakan tare dan nata ba, rahoton jaridar Vanguard.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHDDwKyYp6aZZH52f5Jpb29loqS7orjDqGSnmV1meq6x0qygZqaRYn9uss6rmZ6rXamubrLIrZirZZSWequx0aKlZqulo666sc1msJqmXayutK3NZpuaZaOquKJ5xaJkpK%2BRqLWmecOao6ikmWKubn6Pa2po