Takaitaccen tarihin Uba Sani wanda El-Rufai yake goyon bayan ya karbi Gwamna a 2023

  • Sanata Uba Sani shi ne wanda Malam Nasir El-Rufai yake goyon baya ya zama Gwamnan Kaduna
  • Kusan dai duk wanda ya san Gwamna Nasir El-Rufai a siyasa, to ya san shi ne tare da Uba Sani
  • Kafin zuwansa Majalisar dattawa, Sani yana cikin manyan masu ba Gwamnan Kaduna shawara

Kaduna - Wannan karo mun leka jihar Kaduna, inda mu ka tattaro maku kadan daga cikin tarihin Uba Sani wanda ake tunanin zai rike tutan APC a 2023.

1.Haihuwa

Kamar yadda shafinsa na Wikipedia ya nuna, an haifi Uba Sani a ranar karshe na shekarar 1970. Hakan yana nufin a karshen bana zai cika shekara 52.

An haifi ‘dan siyasar na a garin Zaria da ke Arewacin jihar Kaduna, inda a nan ne ya tashi.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

2.Karatun boko

Bayan firamare da sakandare, Uba Sani ya yi karatun zama Injiniya a jami’a. Daga nan sai ya saki layi, yayi digirgir a fannin tattalin arziki a Uni Calabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baya ga haka, Sani ya samu shaidar PGD a bangaren ilmin kasuwanci a jami’ar tarayya ta Abuja.

Sanatan mai-ci yana cikin wadanda suka yi adawa da gwamnatin soja, suka hura wuta cewa mulki ya koma farar hula. A karshe an yi nasara a shekarar 1998.

A kan haka ne Uba Sani ya kafa kungiyar Movement for Freedom and Justice, ya kuma yi aiki, har ya rike manyan mukami a kungiyoyi irinsu CD da JACON.

4.Shiga siyasa

Ana dawowa mulkin farar hula a 1999, Sani ya goyi bayan takarar Olusegun Obasanjo a PDP. Hakan ta sa ya zama hadimin Obasanjo da ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

An yi ram da mai mulki a Kaduna yana dauke da AK-47 kusa da sansanin ‘Yan bindiga

Baya ga aiki da ya yi a matsayin Mai taimakawa shugaban kasa wajen hulda da jama’a, Sani ya yi aiki da Ministan Abuja, Nasir Ahmad El-Rufai a hukumar FCTA.

5.Takara a PDP

A shekarar 2011, Uba Sani ya nemi zama Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, amma bai yi nasara a zaben fitar da gwani ba, karshe CPC ce ta ci zaben.

6.Gwamnatin Kaduna

Bayan Nasir El-Rufai ya zama gwamna a Mayun 2015, sai ya ya nada Uba Sani a matsayin mai ba shi shawara kan harkar siyasa da sauran harkokin gwamnati.

Da zaben 2019 ya karaso, sai Hadimin ya nuna yana sha’awar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya. Hakan ta sa ya karbe takara a APC, ya doke Shehu Sani na PRP.

7.Majalisar dattawa

Sanata Uba Sani yana cikin wadanda suka fi kawo kudiri a zauren majalisar dattawa. Wasu daga cikin kadarorin da ya gabatar a shekaru uku sun zama doka a yau.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Sani ya kawo kudirin kafa FCE a garin Giwa, da babban asibitin tarayya a Rigasa, da makarantar gandun daji a birnin gwarri da jami’ar fasaha duk a jihar Kaduna.

Sanatan ya kawo kudirin da zai bada damar kafa cibiyar koyar da aikin gona a garin Chikun, da makarantar koyar da fasahar zamani na ICT a kudancin Kaduna.

Daga cikin hadiminsa a majalisar dattawa akwai Bello El-Rufai, babban 'dan Gwamnan Kaduna. Shi ma Bello El-Eufai zai yi takarar 'dan majalisar wakilai a 2023.

Daga Malam sai Uba

A farkon watan nan aka ji labari Mai girma gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya zabi Sanata Uba Sani a matsayin wanda yake so ya zama ‘dan takaran APC.

Zuciyar Malam Nasir El-Rufai ta natsu da Sanata Uba Sani. Shi kuma Sani Abdullahi watau Dattijo ba zai samu tikiti ba, zai yi takarar Sanata ne a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoF3hZZvcGaskaCuqsDAnJqepl2prrO1x6KlZq2Slnq0rc2iZLCZnpmubrHLZqmunpGeerqtyp5koKeppLtursCymKdlqZZ6u63MmmSgr5Giu6K6jKSYna2elnw%3D