A ranar 18 ga watan Disamban 2021, Zarah Buhari Indimi ta samu karin shekara daya kan shekarun ta na haihuwa.
Mijin ta, Ahmed Indimi, ya garzaya shafinsa na Instagram da safiyar Asabar inda ya bayyana yadda ya ke ji game da 'yar kwalisar matarsa yayin zagayowar ranar haihuwar ta.
Kamar yadda ya wallafa:
"Barka da ranar zagayowar haihuwar ki rai mai cike da abubuwan mamaki @mrs_zmbi.Kara karanta wannan
Shugabannin kungiyar ASUU sun dauki matsaya a kan batun sake komawa yajin aiki a Najeriya
"Hadin da ke tsakanina da ke ba a iya musantawa, ba a iya kwatanta da yawan son da na ke miki, shakuwar da ke tsakaninmu da juna ba a iya raba ta. Barka da ranar zagayowar haihuwar ki masoyiya ta."Babu bata lokaci jama'a suka garzaya tare da fara taya ta murnar zagayowar ranar haihuwar ta.
Kara karanta wannan
Sheikh Jingir ya magantu kan karuwar rashin tsaro, ya aike wa 'yan Najeriya muhimmin sako
@mercy_osaghai: "Barka da ranar zagayowar haihuwa ga kyakyawar matar ka. Ina fatan za ta kasance koyaushe cikin farin ciki."A wani labari na daban, surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmed Indimi, ya birge mabiya a kafofin sada zumunta da irin rayuwar soyayyarsa bayan ya rubuta wa matarsa Zahra Buhari kalmomi masu dadi.
Da ya je shafinsa na Instagram, dan hamshakin dan kasuwa ya bayyana yadda yake haukan son matarsa.
Matashin ya wallafa hotonsa tare da Zahra inda ya raka shi da rubutu mai ratsa zuciya wanda ya kayatar da mabiya kafofin sada zumunta.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC3wKelsq%2BfpLFwfZNtb2xuZ2LBosHSmqqapl2grq2tzJqlZqufrq66xcBmm5plkZ26prCMoqWdoZ2eerqtjLOYsrGRo7y4rYyzmKuZmGKvtrTAq6BmqpGjrrN5wZqxnZmpYrGquoytmGg%3D